Connect with us

News

Masu bukata ta musamman sun yi barazanar kai karar INEC kotu

Published

on

Daga yadir sani Abdullah 

 

Masu bukata ta musamman a jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya sun yi barazanar kai hukumar zabe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan korafin kin tanadar abubuwan da suke bukata domin shiga zaben gwamna da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Yuni.

Advertisements
Advertisements

Jaridar Premium Times ta ambato shugaban kungiyar masu bukata ta musamman reshen jihar Ekiti, David Anyaele yana shaida wa ‘yan jarida cewa matukar INEC ba ta yi abin da ya dace ba, za su shigar da kara kotu kan take hakkinsu, da dokokin Najeriya suka ba su a matsayin ‘yan kasa.

Advertisements

Mr Anyaele ya kara da cewa “duk wani yunkuri na hana ‘ya’yan kungiyarmu kada kuri’a zai sa mu kalubalanci INEC a gaban kuliya domin take dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu kan walwalarmu.”

Advertisements
Advertisements

Ya kara da cewa kungiyarsu ta damu matuka kan halin tabarbarewar tsaron da ake fuskanta, musamman yadda ‘yan daba ke hana wasu kada kuri’a. Don haka ya bukaci hukumar zaben ta yi aikin hadin gwiwa da ‘yan sanda domin ba su tsaron da ya dace a lokacin zabe.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending