Connect with us

News

BAYAN JANYE TAKARA, SANATAN APC YA SAUYA SHEKA DAGA JAM´IYYARSA ZUWA PDP

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a majalisar Dattawa ta ƙasa, Sanata Adamu Aleiru, ya yanje daga tseren neman tikitin tazarce kan kujerarsa a APC.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa bayan haka Sanatan ya sauya sheƙa daga APC zuwa babbar jam’iyyar hamayya wato PDP.

Babban mai taimaka masa ta bangaren yaɗa labarai, Abdullahi Zuru, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ta wayar salula.

A kalamansa, Zuru ya ce:”Eh dagaske ne, Aleiru ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP, amma yanzun ina taro ne, zan kira ku daga bayan idan na gama.”

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending