Connect with us

News

Da dumi-dumi: Ganduje ya sauya sunan jam’ar KUST Wudil

Published

on

 Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil KUST da Suna Aliko Dangote
 Jaridar Indaranka ta rawaito Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce ci gaban ya biyo bayan shawarar da kwamitin  da aka tura jami’ar ya bayar.
 Ya bayyana cewa a yanzu za’a rika kiran makarantar da Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST), Wudil.
 Malam Garba ya kara da cewa an mika batun ga majalisar dokokin jihar domin nazarin dokokin da suka kafa jami’ar domin yin gyara.
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending