Connect with us

News

GWAMNANA PLATEAU:MASU NEMAN TIKITIN APC 18 SUNYI WATSI DA ZABEN FIDDA GWANIN JAM´IYYAR

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

Plateau – Masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Plateau a zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka kammala kwanan nan sun yi zanga-zanga a kan bayyanar Nentawe Yilwatda a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

Masu takarar sun nuna rashin jin dadinsu da kin amincewa da zaben fidda gwanin a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren kungiyar manema tikitin na APC a Filato, Danyaro Sarpiya.

Advertisement

 

Jawabin da aka gabatarwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Jos ya yi zargin cewa gaba daya tsarin bai yi daidai da ka’idojin jam’iyyar APC na fitar da ‘yan takara a zaben 2023 ba.

Sun yi kira ga sake nazarin tarukan jam’iyyar daga matakin unguwa don samun damar zaben deleget a tsanake don shiga sabon zaben fidda gwani da zai haifar da sahihin dan takara.

 

“Mun rubuta takardar daukaka kara ga kwamiyin daukaka kara domin magance wannan zambar don kare APC a Plateau.

“Hujjarmu ta daukaka karar ya karkata ga cewar ba a yi zaben deleget ba kuma ana ta yiwa jerin sunayen deleget din kwaskwarima da canjin karshe da aka yi a ranar zaben fidda gwani.

Advertisement

“An kange wadannan deleget da ake magana a kansu daga masu rike da mukaman siyasa da shugabannin kananan hukumomi.

“A yayin zaben fidda gwanin, wasu mutane marasa izini sun kasance a wajen zaben don tsoratar da mutane da bibiyar kuri’un deleget.”

Yan takarar sun tuna cewa sun tabo muhimman batutuwa a taron manema labarai da aka yi a ranar 9 ga watan Mayu, kuma sun sanar da duniya shirin tursasa Yilwatda a kan jam’iyyar.

 

Kokarin jin martanin APC reshen Plateau ya ci tura domin sakataren labarai ta, Sylvanus Namang, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa harkoki sun sha kansa saboda zaben fidda gwanin sanatan APC.

 

Advertisement

Har ila yau, ya sanar da hukuncin da ya yanke a cikin wata wasika wanda aka gabatawar shugaban APC na gundumar Margif/Kopmur da ke Mushere, karamar hukumar Bokkos, wadda aka mika kwafinta ga shugabannin APC na karamar hukuma da na jaha.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending