News
Zargin Almundahanar N2.9bn: Kotu ta umarci EFFC ta ci gaba da tsare Okorocha
Daga khadija Abdullah muhmd
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar gobe Talata don sauraron buƙatar belin da Sanata Rochas Okorocha ya shigar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya tsayar da ranar ne bayan lauyan Okorocha, Okey Amaechi, SAN, ya shaidawa kotun cewa an shigar da bukatar belin wanda yake karewa, biyo bayan karar da ya shigar a gaban kotu.
Ana sa ran karbar bukatar belin Sanatan tare da wanda ake kara, Anyim Nyerere Chinenye, wanda kuma ya shigar da bukatar ta hannun lauyansa, Darlington Onwunzurumba.
Bayan da aka gabatar da karar, lauyan EFCC, Gbolahan Latona, ya sanar da cewa tuhume-tuhume 17, mai kwanan wata 24 ga watan Janairu da a ka tattara sau a ranar 31 ga watan Janairu, na gaban kotu.
Ya kuma roki kotu da ta karanta wa wadanda ake tuhumar laifukan da ake tuhumar su da su domin su samu damar ɗaukaka kara.
Okorocha, Sanata mai Wakiltar Imo ta yamma, wanda shi ne wanda ake tuhuma na 1, an gurfanar da shi ne tare da Chinenye, Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, da Legend World Concepts Limited a matsayin na 2 zuwa na 7.
Ana zarginsa da karkatar da kudade har naira biliyan 2.9 a lokacin da ya ke gwamnan Imo.
Bayan wasu sa’o’i ne sai kuma a ka yi waje da Okorocha zuwa shelkwatar EFCC inda za a ci gaba da tsare shi a can.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
