Entertainment
Davido ya yiwa Bashir Ahmad shagube akan rashin samun tikitin takarar majalisa
Daga kabiru basiru fulatan
Fitaccen mawakin Nigeria, David Adedeji Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yiwa tsohon hidimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bangaren kafafen sadarwa, Bashir Ahmad, shagube akan rashin samun tikitin takarar dan majalisa a yankin Gaya, Ajingi da Albasu dake jihar Kano, wanda ya samu kuri’u 16, yayin da abokin karawarsa, Abdullahi Gaya, ya samu kuri’u 109 a zaɓen fidda gwani na dan majalisar yankin, karkashin jam’iyyar APC.
Wike Ya Caccaki Tambuwal, Zai Goyi Bayan Atiku.
Cikin wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar, tace Davido yayi martani a wallafar da Bashir Ahmad yayi a shafin Twitter, da yake nuna yadda akayi magudi a zaben, inda Davido yace “Karma” was at work “These-called election in Osunnoo KARMA A BITCH” (Ma’ana kamar ace “alhaki kwikwiyo ne” ko kuma “ramuwar gayya tafi ta gayya zafi” sannan yace irin wannan aka kira zabe a Osun) inji Davido.
Tuni dai Bashir Ahmad yayi watsi da zaɓen fidda gwanin, wanda yace cike yake da kura-kurai, domin a matsayin na dan takara, sai barin wajen zaben yayi, saboda yadda aka jibge yan Daba, kuma su kansu masu kada kuri’ar (Daliget) abokan karawarsa ne ya kawo su.
