News
APC ta fada sabon rudani kan batun dan takarar shugaban kasa na maslaha
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fada cikin sabon rudani bayan shugabanta, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa sun amince da shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Bayanai sun nuna cewa Sanata Adamu ya bayyana haka ne a wurin taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC a Abuja ranar Litinin din nan.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC matsayarsu ne bayan ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Ya sanar da wannan mataki ne kwana guda kafin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai jim kadan bayan hakan, gwamnonin Jihohin arewacin Najeriya karkashin jam’iyyar APC sun yi watsi da matsayar shugaban jam’iyyar tasu.
Daya daga cikin gwamnonin ya shaida wa BBC cewa suna nan a kan bakansu na mika mulki ga kudancin kasar a zaben 2023.
Da yake jawabi ga manema labarai a fadar Aso Villa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce Shugaba Buhari ya tabbatar musu cewa bai goyi bayan wani mutum ba cikin mutum 23 da ke son jam’iyyar ta tsayar da su takara.
Ya kara da cewa sun dauki matakin goyon bayan dan takara daga kudancin kasar ne domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasar.
Shugaban APC ya sanar da wannan mataki ne kwana biyu bayan gwamnoni 11 na arewacin Najeriya karkashin jam’iyyar sun amince mulki ya koma kudancin kasar bayan mulkin Shugaba Buhari.
Wannan matakin nan nufin sauran masu neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar ta APC ba su samu tubarrakin jam’iyyar tasu ba.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
