News
Hukumar Yaki ya yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama wasu mutum 18 da Wani Dan hidimar kasa da ake zarginsu da yin barna ta yanar gizo
Daga Yasir sani Abdullahi
Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC) ta kama Dan hidimar kasa da wasu mutum 18 bisa tuhumarsu da yin Danfara ta yanar gizo
Jaridar leadership Hausa ta rawaito cewa an cafke mutum 18 ne a lokoja a jahar kogi
Hukumar tace ta kama dan bautar kasa adamu shu,ibu ne da mutum 18 a wannan makon
Sauran sun hada da Achimugu Ojonoka, Victor Atsumbe, Akoh Grace, Usman Abubakar, Jacob Emmanuel, Solomon John, Christian Oyakhilome, Adesanya Adeolu, Uloko Ojonugwa da Timothy Moses, Negedu Onuchei, Usman Tenimu, Lukman Musa, Samuel Atadoga, Daniel James, Abdulrazaq Ahnod, Olarewaju Olumide da Ademola Daniel.
Bayan kama su, an kwato wata mota kirar Lexus, makudan kudade da ake zargin sun samu ne ta haramtacciyar hanya, nau’ikan wayoyi daban-daban, kwamfutoci da sauran kayayyaki Daban-daban.
Daga karshedai hukumar tace zata gama bincike kafin ta turasu kuliya manta sabo
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
