Connect with us

News

Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

Shugaban hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce siyan gidaje da filaye hanya ce mai sauki da masu satar kudi ke boye dukiyoyinsu.

Rukunin gidaje na ‘Buhari Estate’ na ‘yan sanda ne ba ‘yan bindiga ba – ‘Yan sandan Najeriya

Advertisement

Bawa ya furta hakan ne a jiya a Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Kungiyar Kwararru masu dillancin gidaje da filaye, (NIESV), Emmanuel Wike.

 

Bawa yace “wata daya da ya wuce, mun gano cewa wani ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya ya gina Jami’a a Kaduna kuma babu wanda ya sanar da mu, har mambobin ku. “Don haka, ba zan yi shakkan cewa siyan filaye da gidaje yana daya daga cikin hanyoyi mafi sauki na boye kudi ga masu sata.”

 

“Shi yasa za mu karfafa SCUML da dukkan kayan aiki don taimaka mana sauke nauyin da ke kanmu, duk abin da muke yi doka ta amince da shi, ” in ji shi.

 

Advertisement

Ya bukaci mambobin kungiyar ta NIESV su rika biyayya ga dokar aikinsu na sanar da EFCC duk wani ciniki ko hada-hada kamar yadda ya ke a dokar hana almundahar kudade na 2022.

 

A bangarensa, Wike ya EFCC ta taka rawar a zo a gani wurin gurfanar da manyan mutane da ke aikata rashawa.

 

Ya bada tabbacin cewa mambobinsa za su bawa EFCC hadin kai wurin tona asirin bara-gulbi a cikinsu.

 

Advertisement

Hukumar dai ta EFCC ta sha cafke kadarorin manyan kusoshin gwamnati, wadanda take zargin su da ruf da ciki akan dukiyar talakawa.

 

Ko a kwanakin baya sai da ta kame tsohon Akanta Janar na Najeriya Ahmed Idris bisa zargin sa da badakalar kudade da jimlar adadin su ya kai Naira biliyan 170 tare da bayyana manyan kadarori a ciki da wajen Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending