Connect with us

News

Rukunin gidaje na ‘Buhari Estate’ na ‘yan sanda ne ba ‘yan bindiga ba – ‘Yan sandan Najeriya

Published

on

Daga maryam bashir musa

 

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun mamaye wani rukunin gidaje mai suna Buhari Estate da ta mallaka a yankin Badagry na Jihar Legas.

Tsohon Ministan Harkokin Ƙasashen Waje ya samu tikitin takarar Sanatan Jigawa a PDP

 

Advertisement

Cikin sanawar da fitar a yau Asabar, rundunar ta ce wani mutum ne “da ya yi kama da mai ilimi wanda ya kamata a ce ya san haɗarin yaɗa labaran ƙarya yake yaɗa bayanai da zimmar tayar da fitina” a wani bidiyo, yana iƙirarin cewa ‘yan bindiga ne suka mamaye rukunin gidajen.

 

Sanarwar ta ce rukunin gidajen mallakin rundunar ne kuma jami’an ‘yan sanda ne da iyalansu suka mallake su ta hanyar wani shirinta.

 

“Rundunar ‘yan sanda na shawartar mutane kan muhimmancin tantance abu kafin yaɗa shi don kauce wa tashin hankali, musamman idan aka yi la’akari da mabambantan ƙabilun da ke cikin ƙasa [Najeriya],” in ji rundunar.

 

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending