Entertainment
Khaby Lame ya zama wanda ya fi kowa yawan mabiya a duniyar TikTok
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Haifaffen Senagal kuma fitaccen dan TikTok Khaby Lame ya zama wanda ya fi kowa yawan mabiya a duniya cikin masu amfani da manhajar.
Yana bidiyonsa ba tare cewa kala, yana kwatanta masu amfani da TikTok da na Charli D’Amelio.
A yanzu Khaby na da masu bibiyarsa miliyan 142.8 a manhajar, idan aka kwatanta da D’Amelio’s 142.3
A watan Nuwambar 2020, D’Amelio ta zama ta fi kowa yawan mabiya inda ta haura miliyan 100.
Khaby ya bude shafinsa na TikTok a watan Maris na 2020 yayin annobar korona bayan an kore shi daga aikin kamfani a Italiya.
A shafinsa yana yin bidiyo masu abin dariya da ke nuna yadda ake yin abubuwa masu wuya babu gaira babu dalili.
Advertisements
