Ministocin Sri Lanka sun ce za su tafi Rasha da Qatar a ranar Litinin domin neman fetur mai sauƙi.
2023: Buri na shine na maida Kano cibiyar kasuwancin Afrika — Salihu Tanko-Yakasai
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan gwamnatin ƙasar ta ce man da take da shi ya ƙare, lamarin da ya haddasa farashinsa ya ƙaru a ƙasar.
Ministan makamashi na ƙasar Kanchana Wijesekera ya bayyana cewa suna neman hanyoyin samun sauƙi.
Ko a watan da ya gabata sai da tsibirin wanda ke cikin matsin tattalin arziki ya shigar da mai cikin ƙasar daga Serbia, amma ƴan siyasa a ƙasar sun ce za su yi wa gwamnatin Shugaba Putin magana.
Haka kuma makarantu da ayyukan da su zama dole ba za su rufe na mako biyu a ƙarin mako biyun da suke rufe a halin yanzu.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na Yan Sri Lanka sun samu raguwa a yanayin abincin da suke ci. sakamakon ƙarancin abinci da kuma ƙarin farashi.
