Connect with us

Business

A shirye Ukraine take ta koma fitar da kayan abinci zuwa kasashen Afirka

Published

on

 

Daga Khadija Abdullahi Mahmud

 

 

 

Yawancin kasashen Afirka sun dogara da Rasha da Ukraine wajen sayen kayan abinciImage caption: Yawancin kasashen Afirka sun dogara da Rasha da Ukraine wajen sayen kayan abinci

Advertisement

Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa sojoji za su yi zanga-zanga a Abuja

Ministan harkokin waje na Ukraine, Dmytro Kuleba, ya ce a shirye kasarsa take ta koma ta ci gaba da fitar da hatsi zuwa kasashen Afirka da sauran sassan duniya ba tare da wani sharadi ba, idan har Rasha ta kawo karshen rufe hanyar da ta yi ta teku ( Bahar Aswad).

 

A wata hira da jaridar kasar Tanzania ta, Citizen, ministan ya ce duk da cewa kasashen Afirka da yawa sun kasance ‘yan ba-ruwanmu a yakin mamayar da Rasha ke yi da karasa, Ukraine za ta tabbatar da ci gaba da aiwatar da bangarenta na yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

 

Ya ce, Ukraine, za ta ci gaba da aiki kut da kut tare da dukkanin kasashen Afirka a kwanaki da makonnin da ke tafe domin ta tabbatar dukkanin kayan abincin da aka saya sun kai ga kasuwannin kasashen.

Advertisement

 

Ta kuma yi kokarin kawo karshen karancin abincin da ake yi a duniya, wanda Rasha ta haifar, in ji shi.

 

Mista Kuleba ya bukaci duniya da kuma dukkanin kasashen Afirka da su yi aiki tare su matsa wa Rasha lamba ta bari a rika wucewa da kayan abinci ta ruwa zuwa kasashe.

 

Farashin mai da kayan abinci a Afirka ya yi tashin gwauron-zabi tun daga ranar 24 ga watan Fabrairu, lokacin da yakin Rasha da Ukraine ya barke.

Advertisement

 

Duk wani yunkuri na wasu shugabanni na sassauta lamarin wanda rikicin ya haddasa ya gagara samun nasara.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending