Connect with us

News

Coca-cola da Medshare sun ba da tallafin kayan-aiki na N3bn ga asibitin Aminu Kano

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

A jiya Juma’a ne kamfanin Coca Cola da abokin harkokinsa, Medshare tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya su ka bayar da tallafin kayan aiki na Naira biliyan 3 ga Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Jihar Kano, ƙarƙashin shirin ‘Safe Birth Initiative’, wato Shirin Haihuwa Lafiya , SBI.

Advertisement

FALALAR GOMAN FARKO NA ZULHIJJA.

An ƙaddamar da kayayyakin ne a hukumance tare da miƙa su a wani biki na musamman da aka gudanar a Asibitin dake Kano a jiya.

 

A wajen bikin mika kayan, Babban Daraktan kamfanin Coca-Cola, Alfred Olajide, ya ce an gudanar da shirin ne da nufin inganta rayuwar mata masu juna biyu da kuma rage yawan mace-macen yara.

 

“Shirin Haihuwa Lafiya Haihuwa wani bangare ne na shirin jin dadin kamfanin, don tallafawa kokarin gwamnati na rage yawan mace-macen mata da jariran da ke mutuwa sakamakon matsalolin da suka shafi haihuwa,” ya bayyana.

Advertisement

 

Olajide ya jaddada ƙudirin Coca Cola na tabbatar da lafiya da walwalar mata a matsayin ginshikan al’umma.

 

Ya ce kayan aikin da aka bayar sun haɗa da injinan kashe kwayoyin cuta, na’urorin rainon jarirai, gadajen agajin gaggawa, ICU, injinan hoton sassan jiki Ultrasoumd da dai sauransu.

 

Farfesa Auwal Gajida, Shugaban Majalisar Ba da Shawarar Likitoci ta Asibitin, wanda ya yi alkawarin yin amfani da kayan ta hanyar da ya dace, ya yaba wa kamfanin bisa wannan karamcin.

Advertisement

 

Ya ce wannan karamcin zai taimaka matuƙa wajen inganta sakamakon masu juna biyu da kuma rage yawan mace-macen yara.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending