Connect with us

News

NDLEA ta kama wani matashi bisa zargin safarar marainiya domin fitar da kwaya

Published

on

 

Daga Khadija Abdullahi Mahmud 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wani mutum bisa zargin safarar wata marainiya domin fitar da tabar wiwi zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Advertisement

Yadda Uwargida Za Ta Adana Naman Layya

Jaridar Vanguard a Najeriya ta ruwaito cewa mutumin mai suna Matthew Bassey ya yi yunkurin fita da tabar ne ta hanyar saka ta cikin jakar marainiyar mai suna Peter Eno.

Advertisement

 

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Mr Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce wanda suke zargin ya yaudari yarinyar ne da nufin sama mata aiki a kasar ta Dubai.

Advertisement

 

Hukumar ta ce ta kama kilo 2.80 na tabar wiwi a cikin jakar yarinyar wanda aka boye cikin kayan abinci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending