Sports
Chiina ta hana ‘yan wasan tamaula yin zane-zane a jikinsu ta kuma umarci wadanda keda su da su cire – a sabuwar dokar da ta kafa.
Hukumar da ke kula da wasanni ta kasar ta ce ta hana daukar ‘yan wasa masu zane-zane a jikinsu a babbar tawagar kasar da kuma ta matasan ta.
Hukumar ta ce ta yi hakan ne don kawo da’a da nuna kyawawan dabi’u da halaye da ya kamata matasa su yi koyi da su.
An umarci fitattun ‘yan wasan China ciki har da Zhang Linpeng da su rufe zanen da ke jikinsu da cewar suke sa riga mai dogon hannu da rufe duk wani zane-zane da suka yi.