News
Gobara ta lalata ilahirin ginin Majalisar Wakilan Afrika Ta Kudu
Daga Muhammad zahraddin
Hukumomin kasar Afirka ta Kudu sun ce wata gagarumar gobara da ta tashi a cikin ginin majalisar da ke birnin Cape Town ta lalata majalisar dokokin kasar gaba daya.
Ƴan sanda sun kama wani da ake zargi, tare da gurfanar da shi da laifin fasa gida, da sata.
Wani mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta kasar ya shaida wa gidan talabijin na Afirka ta Kudu cewa gobarar ta sa rufin babban ginin majalisar ya ruguje.
Shugaba Cyril Ramaphosa, wanda tun da farko ya ziyarci wurin, ya bayyana gobarar a matsayin mummunan al’amari.