Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Ma’aurata Bisa Zargin Safarar Wiwi 

Published

on

Picture of skunk seized by NDLEA 750x375

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wasu ma’aurata a ƙauyen Takut da ke ƙaramar hukumar Lapai, bisa zargin safarar ganyen wiwi nau’in skunk mai nauyin gram 118.

A cewar jami’an hukumar, an gano miyagun ƙwayoyin ne a cikin ɗakin girki na gidan ma’auratan, bayan wani samame da suka kai ranar 9 ga watan Afrilu.

Advertisement

KANO: Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Matasa Biyu Bisa Zargin Damfarar Sama Da Mutum 500 Da Sunan Aljannu

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a farkon makon nan, inda ya ce matakin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka samu.

Advertisement

A wani samame daban kuma, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kwato manyan adadin miyagun ƙwayoyi daga wata babbar mota da ke ɗauke da kayan gyaran mota.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da ƙwayoyi 42,290 na Rohypnol, kwalabe 82,700 na maganin kodin, da kuma allurar Pentazocine guda 10,000.

Advertisement

An kama motar ne a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, a yankin Njimtilo na jihar Borno, bayan ta taso daga Nnewi a jihar Anambra.

“Mun kama wanda ake zargi da mallakar waɗannan kwayoyi, Eleje Ibeabuchi mai shekaru 43,” in ji Babafemi.

Advertisement

Hukumar NDLEA ta jaddada kudirinta na ci gaba da yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, tare da gargadin masu hannu a irin wannan haramtacciyar sana’a da su daina ko su fuskanci hukunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending