Connect with us

News

Bauchi: Dakarun Soji Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mata 6 Da Yara 13

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Rundunar Sojan Najeriya ta sanar da samun nasara a wani samame da dakarunta suka kai kan maboyar ‘yan bindiga a jihar Bauchi, a wani bangare na ci gaba da yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce sojoji na 33 Artillery Brigade, tare da hadin gwiwar ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, sun kai farmaki a dajin Madam, inda ake zargin ‘yan bindiga na boye.

Advertisement

NDLEA Ta Kama Ma’aurata Bisa Zargin Safarar Wiwi 

Sojojin sun lalata sansanoni da dama da suka hada da Azuge da Hari, tare da kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu suka tsere.

Advertisement

Haka kuma, dakarun sun ceto mata shida da kananan yara 13, wadanda aka bayyana a matsayin ‘yan uwa na wasu daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifuka.

Sanarwar ta kara da cewa an kwato kayayyaki da dama daga maboyar, ciki har da bindiga kirar AK-47, fakitin maganin tramadol, kayan sanye na jami’an tsaro, da kuma babura da dawakai guda biyu.

Advertisement

Rundunar ta jaddada cewa dakarunta na ci gaba da sintiri da rike wuraren da aka kwace domin hana sake dawowar ‘yan bindiga, tare da tabbatar da tsaro a yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending