News
KANO: Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Matasa Biyu Bisa Zargin Damfarar Sama Da Mutum 500 Da Sunan Aljannu
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta cafke wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar sama da mutum 500 ta hanyar kiran waya, inda suke kwaikwayon “aljannu” domin tsoratar da su su tura kuɗi.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano, an ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 10 ga Afrilu 2026, sakamakon sahihan bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu.
Farashin Kaya Ƙaru Zuwa Kashi 15.38 A Najeriya
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Ahmad Ibrahim mai shekaru 24 da Isma’il Muhammad mai shekaru 22, dukkansu mazauna unguwar Dandinshe da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano.
Binciken ’yan sanda ya nuna cewa matasan na amfani da fasahar sauya murya wajen kiran mutane, inda suke gabatar da kansu a matsayin “aljannu”, tare da yi wa wadanda suka kira barazanar fuskantar cuta idan ba su bi umarninsu ba.
A cewar rundunar, “suna umartar wadanda suka tuntuɓa da su aikata wasu abubuwa, ciki har da tura kuɗi, tare da tsoratar da su da sakamakon ruhi idan suka ƙi.”
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin damfarar fiye da mutum 500, tare da karɓar kuɗaɗe da wasu kayayyaki daga hannun jama’a.
Haka kuma an ƙwato SIM guda 28 da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifukan, yayin da bincike ke ci gaba domin gano sauran waɗanda ke cikin wannan ƙungiya.
Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da bincike tare da tabbatar da gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a gaban kotu.
