Business
Farashin ɗanyen man fetur ya ƙaru da kashi 0.27 cikin 100 zuwa dala 78.34 kan ganga ɗaya
Muhammad Zahraddin
gabanin taron ƙungiyar ƙasashe masu arzikin fetur da ƙawayenta ta Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC+) ranar Talata.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an samu ƙaruwar ce a yau Litinin yayin da aka mayar da hankali kan yawan man da ƙasashe za su ci gaba da fitarwa a sabuwar shekarar 2022.
Rahoton ya nuna cewa farashin samfurin Brent ya ƙaru da 0.72 zuwa 78.34.
Ana kyautata zaton ƙungiyar OPEC+ za ta ba da shawarar ƙara ganga 400,000 na mai da ake kaiwa kasuwa a kullum a watan Fabarairu, a cewar wasu majiyoyi.
Ana alaƙanta ƙaruwar farashin da raguwar fitar da mai daga Libya.