Connect with us

News

Gubar dalma da zinare da ake haƙowa a Zamfara sun kashe yara sama da dubu daya’

Published

on

FB IMG 16413774838750065
Spread the love

Daga Muhammad zahraddin

BBC

Ƙungiyar Likitoci masu bada agaji ta Duniya, Doctors Without Borders, ko Medicines Sans Frontier ta ce aikin da take yi na ceto masu ɗauke da gubar dalma a Jihar Zamfara ya kawo ƙarshe.

A 2010 ne dai, mutuwar yara kusan 400 ta ja hankalin ƙungiyar har ta shiga jihar, inda ta ce ta samu nasarar kuɓutar da mutum fiye da dubu takwas daga lokacin zuwa yanzu.

Dr Peter Ajason na cikin likitocin da ke aiki a ƙungiyar ta MSF a Jihar ta Zamfara kuma ya shaida wa BBC irin nasarorin da suka samu.

Ya ce a watan Maris da Afrilun 2010 ne kungiyarsu ta samu kiran cewa yara na mutuwa a jihar Zamfara ba tare da sanin dalili ba.

Advertisement

Mutanen kungiyarsu sun gudanar da bincike sun kuma gano yara 400 sun mutu a wannan lokacin.

Bayan gwaje-gwaje da aka yi shi ne aka gano cewa gubar dalma ce take janyo musu wannan matsala.

“A 2010 an fi samun masu wannan matsalar Yalgama, bayan nan mutane daga jihar Neja ma sutane sun rika tsallakowa domin neman magani.

Advertisement

“Daya daga cikin illolin da wannan gubar dalmar ke yi a jikin jinin yara shi ne tana mayar da su galhanga, sai yaro ya kai shekara 10 amma baya iya yin abin da mai shekarunsa ya kamata ya yi.”

Wannan matsalar ta na taba kwakwalwa ta yadda mutane da yawa suke ikirariin aljanu ne, kuma babu hadin aljanu da wannan matsala, in ji Dr Peter.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *