Connect with us

News

Hukumar tattara haraji ta Kano ta rabawa ma’aikata 200 takardar tuhuma

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Hukumartattara haraji ta jihar Kano, (KIRS) ta rabawa ma’aikatanta takardar tuhuma sama da mutane 200.

Shugabanhukumar, Abdurrazak Datti Salihi ne ya bayar da wannan takardar tuhumar tun a ranar jumaa da ta gabata, ya yin rangadi da ya yi a ofishin hukumar da misalin karfe 5:20 na yammacin Juma ar.

Advertisement

Takardar da shugaban ya bayar ga ma’aikatan, ta kunshi bayani kamar haka. An lura cewa ba ka kan kujera a lokacin da shugaban hukumar ya kawo maka ziyara a ofishin ka a ranar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021

Bisa la’akari da abubuwan da ke sama, ya kamata ku bayyana dalilin da ya sa baka nan, domin za a dau matakin ladabtarwa a kanka.

Wasu daga cikin ma’aikatan sun bayyana cewar ranar Litinin da Juma a shugaban ya yi rangadi bayan karfe 5 na yamma lokacin wasu sun tashi wasu kuma suna wajen aiki a waje domin duba da cewar aikin na su yawanci ba na zama bane su na yawace-yawace wajen tattara kudaden haraji, Iokacin da ya zo ba mitune shi ne ya dauki sunayen wadanda su ke nan daga bisani wadanda bai same su ba a ka bisu da takardar tuhuma (Query) su sama da dari 200.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *