News
Korona ta kama mutum miliyan daya a Amurka a kwana guda
Daga Muhammad Zahraddin
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce babu wani uzuri da Amurkawa ke da shi na kin zuwa ayi musu allurar rigakafin korona.
Kalaman shugaban na zuwa yayin da kasar ta samu masu dauke da korona miliyan daya a cikin kwana daya.
Wakilin BBC yace Mr Biden ya ce akwai isassun alluran rigakafi da za aiya wa kowa kyauta, akan haka ya yi kira ga Amurkawa miliyan 35 da ba a taba yi wa rigakafin ba da su zo a yi musu.
Ko a Italiya hukumomi na duba yiwuwar saka dokar cewa dole ne ko wane ma’aikaci ya yi rigakafin cutar.
Shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai tabbatar cewa duk wanda bai yi rigakafin korona ba ya fuskanci takura da matsin rayuwa.
A daya waje majalisar Faransar na shirin jefa kuri’ar da za ta ba da damar daukar matakin tursasa al’umma yin rigakafi ko akasin haka.