News
Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari A wani labari na daban
Daga Muhammad zahraddin
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban ‘yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu tare da kare kansa a kan labaran karya da ya dinga yadawa a kasashen ketare kan mulkinsa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban dan a waren IPOB, Nnamdi Kanu, ya kare kansa gaban kotu akan yada karairayi dangane da mulkinsa lokacin ya na kasashen ketare. Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa wacce gidan talabijin din Channels ta nuna a ranar Laraba.