Connect with us

News

2023: Ma su neman Jonathan ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC maƙiyan jam’iyar ne — Kawu Sumaila

Published

on

FB IMG 16415328848461235
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Tsohon Ɗan Majalisa mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Takai da Sumaila a Majalisar Wakilai ta Taraiya, Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce duk waɗanda su ke yunƙurin dawo da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara maƙiyan jam’iyar APC ne.

Ya baiyana cewa ba ƙaramar gazawa ba ce a dawo da Jonathan cikin jam’iyyar APC don a bashi takarar Shugabancin ƙasa.

Kawu Sumaila, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce Jonathan ya taka rawar da ya taka, don haka a bar shi shi kadai, ya na mai cewa APC na da ‘yan takara da suka fi cancanta da ga yankin kudancin kasar nan.

Advertisement

Tsohon dan majalisar, ya ce tura Jonathan ya zama dan takarar APC zai nuna gazawar jam’iyyar ƙarara.

Da yake bayyana masu goyon bayan Jonathan a matsayin makiyan APC, Kawu ya ce APC tana da ‘yan takarar da Suka chanchanta daga yankin kudu wadanda za su iya tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

“Ba na jin wadanda ke ingiza Jonathan ya gaji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a karkashin babbar jam’iyyar mu na yi wa APC fatan alheri. Eh, Jonathan dan dimokradiyya ne wanda ya cancanci a yaba masa.

Advertisement

“Amma ya taka tasa rawar a karkashin PDP. Babu shakka ba za a manta da dattakon da ya nuna ba Wajen amincewa da shan kaye da yayi a matsayinsa na shugaban kasa mai ci kuma ya mika mulki ga ‘yan adawa cikin lumana. Hasali ma ya fi wasu mutanen da yawa dattako a jam’iyyar mu”. Inji Kawu

Kawu Sumaila ya ce idan har APC na da sha’awar ba da tikitin takarar shugabancin kasa a kudancin ƙasar nan, akwai jiga-jigan jam’iyyar da su ka bayar da gudunmawa sosai wajen samun nasarar jam’iyyar tun a Shekarar 2013.

Misali, ya ce, daga Kudu-maso-Kudu, ya kamata a yi la’akari da irin su Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya taba zama Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC sau biyu.

Advertisement

Har ila yau, Kawu ya ce daga yankin Kudu maso Yamma, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya tabbatar da cewa shi ne mataimakin shugaban kasa Buhari tun a shekarar 2015 ya cancanci ya gaji shugabansa.

Ya baiyana cewa Osinbajo na da masaniyar yadda zai jagoranci kasar nan bayan yin aiki kafada da kafada da shugaba Buhari.

Daga Kudu-maso-Gabas, Kawu ya ce karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, “wanda ya yi sadaukarwa da yawa tare da bayar da gudunmawa sosai wajen ganin jam’iyyar APC ta samu karbuwa a yankinsa, yana da chanchantar tsayawa takara a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC. ”

Advertisement

Kawu Sumaila ya ƙara da cewa zamanin kakabawa al’umma Dan takara ya wuce, don haka ya kamata ‘yan tsirarun da ke kira ga Jonathan ya dawo APC da su yi taka tsan-tsan.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *