Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Diaz, Ronaldo, Longstaff, Origi, Cantwell, Coutinho, Traore
Daga muhammad muhammad zahraddin
Liverpool na daf da daukar Luis Diaz, dan wasan gefe dan Colombia mai shekara 24 daga Porto. (Sun)
Cristiano Ronaldo na iya barin Manchester United a ƙarshen wannan kakar wasan idan bai amince da sabon kocin kungiyar na din-din-din da za a nada ba. (Star)
Newcastle ta yi watsi da tayin da Everton ta yi kan Sean Longstaff, dan wasanta na tsakiya mai shekara 24. (Shields Gazzette)
Newcastle da wata kungiyar firimiyar Ingila daya na gasar daukan Todd Cantwell dan wasan tsakiya mai shekara 23 daga Norwich. (Sky Sports)
Ɗan wasan gaba na Liverpool Divock Origi mai shekara 26 da Dominic Solanke, ɗan wasan gaba mai shekara 24 na Bournmeouth na cikin ‘yan wasan da Newcastle ke dubawa domin maye gurbin Callum Wilson wanda ya sami rauni. (Telegraph – subscription required)
Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino a shirye yake ya amince da duk wani tayi na zama kocin Manchester United na din-din-din. (Sun)
Tottenham a shirye take ta sake taya Adama Traore, ɗan wasan gefe mai shekara 25 daga Wolverhampton Wanderers. (Athletic – subscription required)
Da wuya idan Manchester United za ta sake daukan sabbin ‘yan wasa a wannan watan, amma a karshen kakar wasan nan za ta dauko dan wasan tsakiya, inda Declan Rice, dan wasan West Ham mai shekara 22 na kan gaba cikin ‘yan wasan da za ta so dauka. (Talksport)
Arsenal ta yi tayin kudi da dan dan wasa ga Fiorentina domin sayen Dusan Vlahovic, dan wasan gaba mai shekara 21. (Ben Jacobs – CBS