News
Gobara ta tashi a kasuwar Nguru ta Jihar Yobe
Daga Usman Abdullahi jibirin Nguru Yobe
Rahotanni daga jihar Yoben Najeriya na cewa gobara ta tashi a babbar kasuwar Nguru da ke jihar.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa indaranka cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar Asabar.
Sun kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga sashen ƴan takalma da kuma ƴan robobi kuma ta laƙume shaguna ba iyaka.
Tuni dai jami’an kai agaji da kuma na kashe gobara suka isa wajen domin kashe gobarar.
Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa indaranak da faruwar lamarin inda ya ce tuni jami’an kashe gobara da matasa suka haɗa hannu inda suke ƙoƙarin kashe gobarar.
Haka kuma ya tabbatar da cewa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
