News
DUNIYAR MUSULUNCI TA YI BABBAN RASHI
Daga kabiru basiru fulatan
A cikin alhini ina yi wa daukacin al’ummar Musulmi a ko ina a fadin kasarmu Najeriya da sauran yan uwanmu Musulmi a sassan duniya ta’aziyya na babban rashi da muka yi a rana mai falala ta Juma’a 6 ga Janairu 2022. Ya bar duniya da shekara 82.
Allah ya karbi rayuwar Dokta Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba. Tsohon Malami a jami’ar Bayero ta Kano kuma shugaban cibiyar koyar da sunnar Ma’aiki SAW ta Darul Hadith da ke Tudun Yola a Kano.
Wannan babban rashi ne ga jama’ar Kano da Najeriya da duniyar Musulunci. A shekara 31, Dr Ahmad ya yi dawainiyar bada ilimin hadisi, wanda shi ne mabubbuga da madogara ta biyu bayan Alkur’ani Mai Girma a Sharia da Mu’amala.
Dokta Ahmad ya yi hidima, ya bada tarbiyya, sannan ya yada ilimi da da’awa. Ya karantar da jerin duk littafai na Sunnah guda shida. Ya karantar da Muwadda ta Imam Malik, sannan ya karantar da Darimi, Allah ya dauki rayuwarsa yana tsakiyar karatun Bagawi.
Ba shakka mun yi babbar asara. Mu jaridar indaranka muna yiwa al’ummar Musulmi ta’aziyya.
Mu duka almajiran Mallam Ahmad ne, mun fa’idantu da karatunsa da nasihohinsa. Muna addu’a Allah ya karbi bakuncinsa. Allah ya jikansa. Allah ya gafarta masa. Allah ya kyautata bayansa. Magabatanmu Allah ya yi musu rahama.
Nagode