News
Ganduje ya kafa kwamitin da zai hana yara masu karancin shekaru shiga otal
Daga Yasir sani Abdullah
Ganduje ya kafa kwamitin da zai hana yara masu karancin shekaru shiga otal ba tare da iyayensu ba, shan Shisha haramunne, yin iyo tsakanin maza da mata a tafki daya lefi ne, sannan madigo da ayyukan luwadi sun hatamta a Kano
Kwamitin zai kara sa ido kan ayyukan DJ a wuraren bukukuwan aure da wuraren taron, za’a dunga rufe duk wuraren taron da karfe 11 na dare.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da motoci sama da takwas domin gudanar da ayyukan kwamitin.