News
Yajin aikin ‘yan sahu a Kano: Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta soke jarrabawa
Daga kabiru basiru fulatan
Biyo bayan shirin yajin aikin da ‘yan Adaidata Sahu ke yi a gobe Litinin Jami’ar Yusuf Maitama Sule to soke jarrabawar da za ta gudanar da karfe 8 zuwa 11 na safe a gobe Litinin.
Jaridar indaranka taruwaito wanna na kunshe cikin wata sanarwar da shugaba kwamitin shirya jarrabawar Jami’ar Dr Yau Datti ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce kwamitin zai tuntubi shugaban Jami’ar domin yanke hukunci kan makomar sauran jarrabawar da za a rubuta.
Tun kwanaki uku da suka wuce yan Sahun suka raba takardun Kira ga matukan da su shiga yajin aikin mako guda don nuna adawarsu ga sabunta koriyar lamba da hukumar KAROTA ta ce suyi.
Haka kuma tun da yammacin yau Lahadi aka ga sun fara sanya ganye alamar yajin aikin na man daram.