News
Zulum ya nemi da a kyautata albashi da walwalar sojojin Nijeriya
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya yi kira da a kyautata albashi da walwalar sojojin Nijeriya, domin a ƙara musu ƙara musu karsashi wajen kare ƙasar nan.
Zulum ya yi kiran a yayin taron taya Babban Kwamandan Rundunar Soji ta mai riƙon ƙwarya, Abdulwahab Eyitayo, murnar ƙarin girma zuwa Manjo Janar a jiya Lahadi a Maiduguri.
Zulum ya nuna cewa sojin Nijeriya sun sadaukar da ran su, kuma wasu har sun rasa rayukan su waje kare Nijeriya, in da ya ƙara da cewa ya kamata a saka musu a bisa wannan sadaukarwar ta su.
Ya kuma taya Eyitayo murna da sauran ofisoshin da a ka ƙarawa girma, inda ya ce jihar Borno da al’ummar ta na taya su murna.
Gwamnan ya baiyana ƙudurin gwamnatin sa wajen tallafawa sojoji domin samun nasarar yaƙi da ta’addanci.