News
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan adaidaita-sahu sun janye yajin aiki a Kano
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Matuƙa baburan adaidaita-sahu sun janye yajin aikin da su ka fara shi tun a ranar Litinin.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa a ranar Litinin ne dai ƴan adaidaita-sahun su ka tsunduma yajin aiki domin nuna rashin goyon bayan yadda hukumar KAROTA ta ce sai sun biya kudi Naira 8,500 domin sabunta lambar rijista.
Sun kuma koka kan yadda KAROTA ke karɓar kuɗaɗen haraji barkatai a hannun su, musamman ma naira 100 da su ke biya kullum, inda har ranar Lahadi ma sai sun biya, duk da cewa ma’aikatan karɓar harajin ba sa fitowa a ranar.
Sai dai kuma a wata ganawa ta tsawon awanni uku da Shugaban hukumar KAROTA, Bafda Babba Dan’agundi ya yi, tare da lauyoyin ƙungiyoyin ƴan adaidaita-sahun, Barista Abba Hikima da Barista Muhammad Dalhatu, an cimma matsaya tsakanin ɓangarori biyun.
Bayan ganawar ne, sai dukkan ɓangarorin su ka kira taron manema labarai, inda a nan ne su ka sanar da cewa an janye yakin aikin.
Sun kuma nuna cewa matuƙa baburan adaidaita-sahun su fito su ci gaba da aiki a gobe Alhamis, bisa doron doka da oda.
Sun kuma baiyana cewa batun N8,500 na sabunta lambar rijista, za a duba shi, inda Dan-Agundi ya ce zai tuntubi gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje don ganin an rage farashin, ko kuma a bar su su biya a tsitstsinke.
Ya kuma ci alwashin samun kyakkyawar alaƙa tsakanin jami’an KAROTA da matuƙa adaidaita-sahun.