Connect with us

News

Majami’a ta rufta tare da kashe mutane 10 a Delta

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Wani ginin gidajen majami’a na Salvation Ministry, Okpanam, a karamar hukumar Oshimili ta Arewa, a jihar Delta, a Kudu maso Kudancin Najeriya, ya ruguje, tare da danne masu ibada da ba a tantance adadinsu ba.

Politics Nigeria ta rawaito cewa, sama da mutane 10 a ka zargi sun mutu a cikin ginin.

Rahotanni na cewa, ginin da aka fara amfani da shi a karon farko, ya ruguje ne da misalin karfe 5:55 na yammacin ranar Talata.

Advertisement

An ceto mutane 8 ba tare da sun ji rauni ba, yayin da a ka garzaya da mutane hudu asibitin kwararru na Asaba, domin kula da lafiyarsu.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *