News
Ɓangaren Gwamna Ganduje ya sake shan kaye a kotu
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
A Najeriya, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da ɓangaren Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na jam`iyyar APC ya gabatar cewa ta jingine hukuncin da ta yi, wanda ya tabbatar da zaben shugabannin jam`iyyar da tsagin tsohon Gwamna Senata Ibrahim Shekarau ya gudanar.
Tun da farko, kotun ta bai wa tsagin Sanata Shekarau gaskiya, amma sai tsagin Gandujen ya nemi ta sake nazarin hukuncin da ta yi.
Kotun ƙarƙashin Mai Shari`a Hamza Mu`azu, ta ƙi amincewa da bukatar da tsagin Gwamna Ganduje ya gabatar saboda ba shi da hurumin gabatar da irin wannan bukatar, kasancewar ya daukaka kara a wata kotun.
Kotun ta tabbatar da hukuncin da ta yi cewa zaben da ɓangaren Shekarau ya yi na shugabannin jam`iyyar a matakin kananan hukumomi yana nan daram, kuma suna da `yancin zabar shugabannin jam`iyyar APCn na jiha.
Barrister Duru Marcel na cikin lauyoyin da ke tsaya wa tsagin Gwamna Ganduje, ya faɗa wa BBC Hausa cewa a irin tasu fahintar hukuncin ya yi musu dadi:
“Muna farin ciki kwarai saboda abin da doka ta fada kenan. Kotun ba ta da hurumin sauraron bukatar da muka gabatar, kasancewar mun daukaka kara game da hukuncin da ta yanke tun da farko. Kuma har an mika wa kotun daukaka kara bayanin hukuncin. Kotun daukaka kara da ke Abuja ce kadai za ta saurari wannan bukatar, kuma muna jiran ranar da za ta sa don sauraron karar.,” in ji shi.
Shi kuwa tsagin Senata Ibrahim Shekarau, cewa ya yi shi ne ainihin wanda ya yi nasara a wannan hukuncin da babbar kotun tarayyar ta yanke.