Connect with us

News

Omicron: Ba za mu dakatar da yin Ummara ba duk da dawowar korona — Saudiya

Published

on

FB IMG 16420980479047085
Spread the love

Daga yasiY sani Abdullah

 

 

Advertisement

Ma’aikatar Hajji da Ummara a Saudi Arebiya ta musanta jita-jitar da a ke na cewa za a dakatar da aikin Ummara sakamakon ƙaruwar annobar korona, bayan zuwan sabon nau’in cutar mai suna Omicron.

Wata majiya a ma’aikatar ta shaidawa shafin yanar gizo na Haramain Sharifain cewa Maikatar ba ta da niyyar dakatar da ummar, amma dai ta na kira ga baƙi da alhazan Ummara da su kiyaye da matakan kariya da mahukunta su ka ɓullo da su.

A kwanannan me dai Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Guda Biyu ya dawo da tsarin bada tazara da juna da kuma sanya takunkumin fuska a Masallatan biyu masu tsarki bayan ƙaruwar cutar ta koron.

Advertisement

“Mu na kira ga duk wani alhaji da masu ziyara da su kiyaye da matakan kariya na bada tazara da juna da sanya takunkumin fuska. Hakan zai tabbatar mana da kariyar kan mu da ta yan’uwa,” in ji Limamin Masallacin Harami na Makka, Sheikh Yasir Al Dossary a sallar Azahar ta yau.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *