Connect with us

News

Garba Shehu: Abin da ya sa gwamnatin Buhari ta sasanta da Twitter

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

A ranar Laraba ne gwamnatin Najeriya ta sanar da janye haramcin da ta saka wa Twitter a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar wa da BBC cewa daga yanzu babu wani sauran korafi da wani daga cikin bangaren ke da shi.
Tuni da dama masu amfani da shafin na Twitter suka tabbatar budewar shafukansu, da suka shafe watanni suna kewa.

Advertisement

Tun a watan Yunin 2021 ne gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da Twitter a fadin ƙasar, bayan ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa tashe-tashen hankali.
Hakan ya haifar da martani mai zafi daga ‘yan Najeriya da dama da suke kallon matakin a matsayin take hakkin bil adama, amma kuma gwamnati ba ta nuna wata damuwa ba, inda ta bar shafin na Twitter a kasar ya ci gaba da kasancewa a toshe.

A hira da BBC mai magana da yawun Shugaba Buharin ya ce kamfanin Twitter ya cika sharudan da gwamnatin Najeriya ta gindaya masa, da suka hada da taimaka wa a yaki miyagun laifuka, da kuma bude ofishi tare da ajiye wakili da gwamnatin za ta rika tattaunawa da shi idan bukatar hakan ta taso.

” Twitter ta amince ta hada kai da Najeriya don a yaki mutanen da ke amfani da kafafensu don jawo kiyayya, kyamar juna, fitina, addini, kabilanci da kuma kawo tashin hankali a kasar Najeriya baki daya,” in ji Garba Shehu.
Ya kara da cewa ” Twitter ta yadda za ta yi aiki da dukkan dokokin Najeriya, kuma za ta bude ofishi wanda zai yi rajista a nan Najeriya wanda yake ko da matsala ta faru tsakanin Twitter da ‘yan Najeriya ga wakilinsu za a iya zama a tattauna.”
Bugu da kari Malam Garba Shehu ya ce daga yanzu Twitter za ta rika biyan haraji kamar yadda suke biya a kasashen Turai.
Ya ce irin arzikin da kamfanin sada zumuntar ya samu a Najeriya ya dace a ce yana biyan kudaden haraji masu yawa, inda ya ce irin kudin da Twitter ke samu akwai inda “raba dai-dai suke yi da wasu gwamnatocin kasashen Turai.”
‘Yan Najeriya da dama sun shafe yammacin Laraba suna bayyana irin shaukin da suke ji tare da abokansu, na mayar da shafin Twitter da suka shafe kusan wata bakwai suna jiran tsammani.
Gwamnatin Najeriya ta rufe Twitter, jim kadan bayan da kamfanin ya goge kalaman Shugaba Muhammadu Buhari game da daukar mataki kan ‘yan kungiyar ‘yan awaren IPOB da ke tada zaune tsaye a kudancin kasar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *