News
Kano: Dokar hana goyo a babur na nan daram — Rundunar Ƴan Sanda
Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta jaddada cewar, har yanzu dokar hana goyo a babura masu ƙafa biyu ta na nan daram a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya baiyana hakan a ranar Alhamis, bayan janye yajin aikin ƴan adaidaita-sahu da su ka yi na tsawon kwanaki uku.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa, bayan da matuƙa baburan adaidaita-sahu su ka tafi yajin aiki a ranar Litinin, kwatsam sai a ka ga wasu na haya da baburan su, inda hakan ya fara firgita al’ummar jihar cewa ƴan Achaba za su dawo.
Da ya ke zantawa da manema labarai, DSP Kiyawa ya ce dokar hana goyo a babur, wacce gwamnatin jihar ta kafa a 2013, tana nan daram.
Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda ta baza jami’anta, domin tabbatar da dokar, saboda haka al’umma su kiyaye.”