News
Firamimistan Burtaniya ya nemi afuwar Sarauniyar Ingila
Daga Yasir sani Abdullah
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya nemi afuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth, saboda wasu shagali da suka gabatar wanda ya saɓawa ka’idojin da aka sa na yaƙi da korona wadanda aka gudanar a na makokin Korona.
Kakakin Mista Johnson ya bayyana shagalin da aka yi yayin da kasar ke cikin halin jimamin mutuwa a matsayin abin takaici.
Ko a lokacin da aka yi jana’izar Yarima Philip, an nuna Sarauniyar zaune ita kadai, domin mutunta dokar ba da tazara.
Mista Johnson dai na fuskantar matsin lambar ya ajiye aiki, amma a farkon makon nan, ya nemi afuwa kan halartar wani taro da a ka yi a 2020 a lokacin da kasar ke cikin halin kullen korona.