Sports
Afcon 2021: Alkalin Zambia Janny Sikazwe da ya bushe wasa lokaci bai cika ba
Daga muhammad muhammad zahraddin ( INDARANKA)
Hukumar ƙwallon Afirka ta yi watsi da koken da Tunisia ta shigar gabanta game da wasanta da alƙali ya bushe lokaci bai cika ba a ranar Laraba.
Caf a cikin sanarwar da ta fitar ba ta yi ƙarin haske ba game da koken da kuma dalilin yin watsi da shi.
Amma hukumar ta tabbatar wa Mali da nasara ci 1-0, da aka ci a wasan.
Ana minti 85 da wasa alƙalin ya bushe wasan, kafin ya ankara ya ce a ci gaba.
Sannan alƙalin wanda aka ce tsananin zafin rana ne ya shafe shi ya sake bushe wasan kafin lokaci ya cika.
Tun a fili Tunisia ta rashin jin daɗinta, inda hukumar Caf da ke shirya gasar ta nemi a dawo bayan an yi minti 20 da bushe wasan domin a ida cika lokacin ya rage.
Tagawar Mali ta fito ammaTunisia ta ƙaurace. Rudanin da aka samu ya haifar da tsaikun soma wasan Mourtania da Gambia.
Manyan wasannin da ya yi alƙalanci
Alƙalin Janny Sikazwe ɗan ƙasar Zambia yana cikin manyan alƙalai a Afirka.
Tun 2007 yake alƙalanci a wasannin Fifa.
Ya taba hura wasanni a gasar cin kofin Afirka a Rasha. Ya kuma hura wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika a 2017.
A 2016, Sikazwe ne ya yi alƙalancin wasan Real Madrid da Kashima Antlers a gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon kafa.
Ya sha hura manyan wasanni a Afirka da suka ƙunshi na ƙungiyoyi da kuma ƙasashe.
Ya hura wasannin rukuni na gasar cin kofin duniya a 2018, wasan Belgium da Panama da kuma wasa takanin Japan da Poland.