Connect with us

News

Da Dumi-Dumi: An yi garkuwa da daliban jami’ar tarayya ta Nasarawa

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

An yi garkuwa da wasu daliban jami’ar tarayya dake garin Lafia a jihar Nasarawa a kusa da harabar jami’ar.

Majiyar Daily Trust ta rwaito cewa, Majiyarmu ta bayyana cewa, an sace daliban ne a unguwar jami’ar da ke Maraba.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an sace dalibai hudu.

Advertisement

Ya ce, ‘yan bindigar sun far wa jama’ar jami’ar ne da misalin karfe 11:30 na ranar Alhamis inda su ka garzaya da daliban zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

“Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Abdul Rahman, a madadin shugabannin hukumar, ya nuna matukar bacin ransa game da wannan abin takaici, ya kuma yi Allah wadai da shi da kakkausar murya da bukatar a gaggauta sakin wadanda aka sace.”

Ya yi nuni da cewa, an samar da karin matakan tabbatar da isassun tsaron rayuka da dukiyoyi a ciki da wajen Jami’ar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *