News
Shekara 2 bayan hamɓare gwamnatinsa, tsohon shugaban ƙasar Mali, Boubacar Keita ya rasu
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Tsohon Shugaban Ƙasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita ya rasu a yau da safe, in ji iyalin sa.
Keita ya rasu a babban birnin ƙasar, Bamako, inda ya rasu ya na da shekara 76.
Keita dai ya hau mulkin ƙasar a shekarar 2013 har zuwa 2020 lokacin da sojoji su ka hamɓare gwamnatinsa.
Wata majiya daga iyalan mamacin ta ce Keita ya rasu a yau da misalin ƙarfe 9 na safe a asibiti.