Connect with us

News

YANZU-YANZU: Buhari ya baiwa sojoji umarnin gamawa da ƴan ta’adda a Naija

Published

on

FB IMG 16422460817653375
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa sojoji umarnin anfani da karfi su gama da ƴan ta’adda masu garkuwa da mutane da kashe-kashe a Jihar Naija.

Mataimakin Shugaban Ƙasa ta Bangaren Kafafen Yaɗa Labarai, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, ya ce shugaban ƙasar ya bada umarnin ne ga Shalkwatar Sojoji ta ƙasa.

Ya ce Buhari, a matsayin sa na Babban Kwamandan Tsaro a ƙasa, ya bada umarnin sojoji su fara fatattaka ƴan ta’addan a Naija, jihar da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji da kuma Boko Haram da ke mamaye wasu sassa na Arewa.

Advertisement

A sakon sa ga gwamnati da al’ummar jihar, Buhari ya nuna jaje da rashawa ga jihar sakamakon hare-haren ƴan ta’adda da su ke fama da shi na kwanan nan.

Ya ce Buhari ya nuna cewa harkar tsaro na bukatar dukkan al’umma ta tallafawa jami’an tsaro, inda ya ce “ta hadin kai da goyon baya ne za mu iya maganin matsalar nan baki daya.”

“A shirye Gwamnatin Taraiya ta ke ta ƙarfafa tallafi da haɗin kai ga dukkan jihohi. Na tabbata idan ƴan ƙasa su ka bada goyon baya, tabbas za mu kawo karshen wannan matsaloli.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *