Connect with us

News

Ɗantata ya zubar da hawaye kan matsalolin Nijeriya

Published

on

FB IMG 16424245657726993
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

Fitaccen attajirin nan na Jihar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, ya zubar da hawaye a wajen ƙaddamar da wani littafin da ya ɗauki nauyin fassarawa a Jami’ar Bayero Kano, BUK.

Ɗantata, mai shekaru 94 a duniya, ya zubar da hawayen ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a gurin taron, wanda a ka gudanar ranar Asabar a BUK.

A cewar sa, matsalolin ƙasar nan kullum ƙara ƙaruwa su ke yi, kuma shugabannin ƙasar babu ruwansu da halin da ƴan ƙasar su ke ciki.

Advertisement

Ya ce abun takaici ne yadda a ke kashe mutane a kullum a kasar nan, kuma shugabannin, a kowanne mataki sun gaza ɗaukar matakin da zai daƙile matasalolin rashin tsaron.

Ɗantata ya kuma ce ba ya ga matsalar tsaro, akwai matsaloli masu tarin yawa da su ka yiwa talakawan ƙasar nan katutu, musamman matsalar tashin hauhawar kayan masarufi da sauran kiyan amfanin yau da kullum .

Sabo da haka, Attajirin ya buƙaci shugabanni da su ji tsoron Allah su riƙa yin abin da zai saukakawa al’ummarsu, in da ya ƙara da cewa su sani Allah zai tsayar da su ranar kiyama ya tambaye su a kan yadda su ka bari a ke kashe mutane babu gaira babu dalili.

Advertisement

“Yanzu bana tsoran kowa, kuma ba na tsoron komai akwai abin da nake so shi ne in mutu ina musulmi kuma in cika da kalmar shahada don na hadu da mahaliccina salun alun”. Inji Ɗantata

Dattijon ya ce, su ma mutane su ji tsoron Allah su gyara halayensu, su sasanta da junansu, inda ya nuna cewa duk wanda yansan ya ci hakkin dan uwansa, ya yi ƙoƙari su sasanta tun kafin su je Lahira.

Da ga nan ne sai Ɗantata ya ƙara fashewa da kuka sabo da halin da yankin arewa ya samu kansa a ciki

Advertisement

Yana zubar da hawaye, Alhaji Aminu Dantata ya ce Allah bazai gyara mana ba har sai mun gyara da kan mu, in da ya ƙara da cewa shi ba abin da bai gani ba a duniya domin shekarunsa 94.

A jawabin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Dr Sa’adu Abubakar lll, ya yi wa al’ummar Kano ta aziiyyar mutanen da su ka rasu a wannan lokacin, har ya roki Alhaji Aminu Dantata a.kan ya jagoranci tattara ilimin Dr Ahmad Bamba na BUK guri guda, wanda ya gabatar a lokacin rayuwarsa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *