Interview
Dalilin Da yasa na ajiye Digiri na a Chemistry na Koma Sana’ar Wainar Fulawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Bayan ya kammala dirigi a jami’a, matashi ya koma soya wainar fulawa a Kano
Hausawa dai sun ce “Sana’a sa’a rashin sana’a sata”. Sannan Hausawa sun ƙara cewa “Sana’a maganin zaman banza”. A kwai kuma karin maganar da Bahaushe kan ce “Girman kai rawanin tsiya”.
Wani matashi mai suna Abubakar Umar Usman, ɗan unguwar Chiranci, Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, ya dogara ne da sana’ar soye-soye domin ya tsira da mutuncin sa.
Shi dai Usman, wanda ya kammala digirin sa a fannin kemistri a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, a shekarar 2017, ya ce ya yanke hukuncin tsayawa da ƙafarsa ne domin ya daɗe ya na neman aikin gwamnati amma bai samu ba.
Bayan da ya kammala shirin bautar ƙasa, wanda a ka fi sani da NYSC, Usman ya nemi aiki a ma’aikatu da dama a faɗin ƙasar nan amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.
“Sana’a maganin zaman banza” in ji Hausawa, hakan ne ya sanya Usman ya yi tunanin ya fara sana’ar sayar da wainar fulawa domin ya riƙa samun kuɗin shiga don ya rufaawa kansa asiri.
“Kamar wasa, sai na yi tunanin na fara soya wainar fulawa ina sayarwa. Sai kuwa na fara. Ban yi tunanin ni mai digiri bane, kawai na fara soya wainar fulawa a kofar gidan mu.
“Kamar wasa, sai na fara jan hankalin kwastomomi. Ƴan mata da matan aure, kai har ma da masu aure da angwaye suna zuwa su siya kullum. Har ta kai ta kawo ma wasu masu auren sun mayar da gurin da nake suyar gurin hirar su,” in ji Usman.
Usman ya ƙara da cewa da ya ga kasuwar ta sa kullum haɓaka ta ke, sai ya kama wani shago, inda ya ci gaba da sayar da wainar fulawa, sai ma ya haɗa da wainar shinkafa da miya, indomi, awara, shinkafa da sauran su.
A hirar da ya yi da Abubakar yace, ya buɗe wajen sayar da abinci mai suna AU Square, ya ce kwata-kwata ba ya jin kunyar sayar da abincin, in da ya ƙara da cewa “suma ƴan matan burge su na ke yi.”
Usman ya ce yana da ma’aikata da su ke aiki a ƙarƙashin sa, har ma da waɗanda ya ke biya naira dubu 12 a wata a kusan shekara uku kacal da fara sana’ar.
Ya ƙara da cewa shi yanzu abinda ya ke samu a sana’ar ta sa ko aikin gwamnatin ya samu, ba kowanne ne zai samu kuɗin kamar yadda ya ke samu a sayar da abinci ba.
“Ni fa ma’aikatan gwamnati da ma na maikatu masu zaman kan su ba kowane zai fini samu ba. Gaskiya dai rayuwa alhamdulillah, asiri ya rufu. Ni ba na ma tunanin sake neman aiki a halin yanzu,”
Usman ya ƙara da cewa shi burin sa ya sake bunƙasa sana’ar sa ya zamana ya bada gudunmawar sa ga tattalin arziƙin Jihar Kano da ƙasa baƙi ɗaya.
@Jaridar indaranka