Gwamnatin Ghana ta musanta cewa tana duba yuwuwar kafa cibiyar karbar masu neman mafaka na Birtaniya.
Kafofin yada labarai da yawa na Birtaniya sun ruwaito cewa Birtaniya na tsara yadda za ta tura dubban masu neman mafaka zuwa kasashe irin su Ghana da Rwanda domin tsugunar da su a can karkashin wani shiri da aka yi wa lakabi da Ingilishi “Operation Dead Meat”, wanda ke nufin kamar kawar da ”Mushe”
A wani sakon tuwita ma’ikatar harkokin waje ta Ghana ta ce ba ta yi wata tattaunawa da Birtaniya ba a kan batun kuma ba ta da niyyar yin wani abu kamar haka a nan gaba.
A shekarar da ta gabata Rwanda ta ce duk da cewa ta kulla yarjejeniyar karbar masu neman mafaka da kasar Denmark, ba ta cikin wannan shiri na Birtaniya.
A shekarar da ta wuce kungiyar tarayyar Afirka ta nuna kin yardarta da shirin mayar da masu neman afuwa daga Turai zuwa Afirka, tana mai cewa shiri ne na kyama wanda ba za a amince da shi ba sam.