News
Takarar Gwamna: Ina jiran lokacin Allah domin Shine mai bada mulki — Gawuna

Daga kabiru basiru fulatan
Mataimakin Gwamnan Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce batun takarar gwamnan Jihar Kano a 2023 abu ne na lokaci, in da ya ce komai Allah ne mai yi.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa, yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023, ƴan takara da dama a jam’iyar APC mai mulki a Jihar Kano na nuna buƙatar su ta tsayawa domin gadon buzun gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Sai dai kuma, wannan jarida ta gano cewa kawo yanzu, ba a ga wata alama ta tsayawa takara da ga wajen Gawuna ba, duk da cewa bisa al’adar siyasa, shi ne ya kamata ya gaji uban gidansa, Ganduje a 2023.
Amma, a wani shiri da Gidan Rediyon Freedom Kano, mai taken “An tashi lafiya”, an jiyo Gawuna na cewa ita magana ta siyasa ko muƙami, abu ne da Allah ne Ya ke yi.
A cewar Gawuna, ban da Allah, babu wanda zai iya baiwa wani muƙami, inda ya ƙara da cewa duk wanda ya kaɗai kugen siyasa da wuri ya san Allah ne ke yi, haka-zalika wanda ya jira sai nan gaba shima ya san Allah ne ke yi.
“Ita maganar siyasa ko maganar muƙami, kowa dai ya san Allah ne Ya ke yi. Banda Allah ba bu mai yi kuma a kwai lokaci.
“Wanda ya buga kugen sa da wuri ya sani, wanda kuma ya bari ya jira lokacin Allah, shima kuma ya sani.
“Mu na jiran lokacin Allah, Allah kuma Shi ne mai yi,” in ji Gawuna.
Gawuna shine kuma Kwamishinan Noma da Albarkatun ƙasa na Jihar Kano.