Connect with us

News

An gano gawar yarinyar da aka sace a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ranar 4 ga watan Disamban 2021.

Published

on

FB IMG 16426939424799555
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

An gano gawar yarinyar da aka sace a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ranar 4 ga watan Disamban 2021.

Mahaifin yarinyar ya tabbatar wa da BBC cewa an gano hakan ne ta hanyar gano wanda ya sace ta ɗin, bayan da ya zayyana wa jami’an tsaro yadda komai ya wakana.

Mahaifin Hanifa ya ce a yanzu haka an tono gawar ƴar tasa wacce mutumin da ya sace ta ya kashe ya kuma binne ta tun kwana biyar da sace ta.

Advertisement

Wanda ake zargi da kisan na gaban ƴan sanda yana fuskantar tuhuma, kuma tuni ya fara bayani kan yadda aka yi ya kashe ta.

Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani kan yadda hakan ta kasance.

Waiwaye

A ranar wata Asabar 4 ga watan Disamban shekarar da ta ƙare ta 2021 ne aka sace Hanifa mai shekara biyar a birnin Kano ranar Asabar, a unguwar Kawaji.

Advertisement

Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma A daidaita-Sahu.

Iyayen Hanifa sun ce mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

“Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu,” a cewar Suraj Zubair, kawun Hanifa.

Advertisement

“Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a A daidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida.

Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *