News
Ghana. Ana ci gaba da ceto wadanda fashewar wata mota ta rutsa da su
Daga muhammad muhammad zahraddin
Mutane da dama ne suka mutu a garin Apiyate da ke yammacin kasar Ghana yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon tashin wata mota makare da wasu abubuwan fashewa.
Rahotanni sun ce motar da ke kan hanyarta ta zuwa wani wurin hakar ma’adinai ce ta yi karo da wata mota yayin da take kokarin kaucewa wani babur da ya shiga gabanta, lamarin da ya janyo fashewar a kusa da garin Bogoso.
Wasu hotunan bidiyo sun nuna gidaje da shaguna dama da suka rushe baya ga mutane da dama da ake zakulowa daga wurin da lamarin ya faru.
‘Yan sandan dai ba su tabbatar da adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba, to amma wata majiya a garin ta ce ya zuwa yanzu an gano gawar mutum 17, to amma akwai yi wuwar adadin zai zarta haka. Masu aikin ceto dai na ci gaba da neman wadanda baraguzan gini ya binne, sannan kuma an sanar da mutane a kan su bar wajen da lamarin ya faru.
Kazalika ‘yan sandan sun yi kiran da a bude azuzuwa da kuma majami’un da ke yankin domin kai wadanda aka ceto.
Lamarin dai ya afku ne da rana in da mutane na cikin harkokinsu sai kawai suka ji karar fashewar wani abu.
Wata mata dake zaune a wani gari dake makwabtaka da Apiyate ta shaida wa BBC cewa a halin yanzu mazauna yankin dama makwabtansu duk sun bar wajen ba a san in da suka je ba.
Tuni dai shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo Addo, ya aika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, tare da yin jaje ga wadanda suka jikkata.
Kazalika shugaban kasar ya sha alwashin cewa gwamnati zata tallafawa al’ummar garin da lamarin ya faru.
Ba kasafai aka fiye samun afkuwar irin wannan iftila’i ba a kasar ta Ghana, to amma wasu al’ummar kasar na diga ayar tambaya a kan irin matakan kariyar da ake da su a wajen jigilar irin abubuwa kayan fashewa musamman a yankin da ke da da yawan wurin hako ma’adina