Connect with us

News

Ba abinda zai dawo da ni harkar siyasa — Obasanjo

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo a ranar Asabar ya sake jaddada ƙudurinsa na ficewa daga harkokin siyasa, inda ya ce babu abin da zai sa ya koma harkar siyasar jam’iyya.

Obasanjo ya baiyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawar sirri da ‘yan Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar PDP na ƙasa a Abeokuta.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya gamsu da zama dattijon ƙasa, inda ya kara da cewa babu abin da zai sa ya koma siyasa.

Advertisement

“Ina so in jaddada cewa yanzu ba na cikin harkar siyasa kuma babu wani abu da zai dawo da ni siyasa.

“Zan kasance mai sha’awar abin da ke da kyau ga Najeriya kuma duk wanda ke son samun shawarata, zan ba shi musamman don amfanin Najeriya da kuma maslahar Afirka.

“Wannan shine dalilin da ya sa nake da irin nauyin da nake da shi a yanzu a Afirka, wanda ba abu ne mai sauki ba,” in ji tsohon shugaban.

Advertisement

Sai dai ya ce PDP za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihin rayuwarsa saboda ya kai matsayin shugaban ƙasa a dandalin jam’iyyar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *